BAMBANCIN DUNIYA DA LAHIRA

BAMBANCIN DUNIYA DA LAHIRA

  • BAMBANCIN DUNIYA DA LAHIRA


DUNIYA: babu tabbas
LAHIRA : akwai tabbas

DUNIYA: akwai mutuwa
LAHI

RA : babu mutuwa

DUNIYA: akwai samu idan aka rasa
LAHIRA : babu samu idan aka rasa

DUNIYA: akwai rashi idan aka samu
LAHIRA : babu rashi idan aka samu

DUNIYA: karya ce
LAHIRA : gaskiya ce

DUNIYA: akwai najasa
LAHIRA : babu najasa

DUNIYA: tana gushewa
LAHIRA : bata gushewa

DUNIYA: akwai tsanani ga muminai
LAHIRA : akwai dadi ga muminai

DUNIYA: akwai dadi ga mushrikai
LAHIRA : akwai tsanani ga mushrikai

DUNIYA: masu tsoron Allah sune ake wulakantawa
LAHIRA : masu tsoron Allah sune ake girmamawa

DUNIYA: mafi yawan masu kudi suna cikin jindadi
LAHIRA: mafi yawan talakawa suna cikin jindadi

DUNIYA: gidan da ba'a bambanta mumini da kafiri
LAHIRA : gidan da ake bambanta mumini da kafiri

wannan shine kadan daga cikin bambancin duniya da lahira,
ya kai 'dan uwana a musulunci, ina maka nasiha da kaji tsoron Allah kayi adalci a cikin addininka ka guji zalunci, domin zalunci yana kama da shirka, ka guji karya domin tana kama da bautawa gumaka.

ya kai musulumi ka sani cewa ba zaka zama mumini ba, har sai ka kasance kamar haka:

1 sai kaji tsoron Allah a cikin sallar ka
2 sai ka hakura da yawan wasanni
3 sai ka zama mai bada zakka
4 sai ka kiyaye farjin ka daga zina
5 sai ka zama mai alkawari
6 sai ka zama mai amana
7 sai ka zama mai kiyaye sallolinka

haka kema 'yar uwa sai kin kiyaye da wadannan abubuwan sannan zaki zama mumina kuma kamilar mace a cikin al'umma sannan kuma ki zama uwa ta gari

Allah yasa mu dace, idan ka samu dama ka tura wannan bayanin zuwa, wasu al'umma, yin hakan zai sanya ka samu lada mai yawa a wajen Allah, domin ka yada abun da yake mai kyau, amma idan baka tura ba babu laifi a gareka, sai dai kawai ka zama marowaci, kuma ka zama daga cikin wadanda basa hani da mummuna, kuma basa umarni da kyakkyawa,

Ya Allah kajikanmu ka yafe mana kura-kuranmu kada ka sanya riya a cikin ayyukanmu

WASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAH WA BARAKATUHU
..

Berlangganan update artikel terbaru via email:

0 Response to "BAMBANCIN DUNIYA DA LAHIRA"

Post a comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel