Gamsassun Mu'ujizozin Annabi (S.A.W)

Gamsassun Mu'ujizozin Annabi (S.A.W)

DAGA CIKIN MU'UJIZOJIN MANZON ALLAH S.A.W MUTANE 1400 SUN SHAN RUWA A RIJIYAR DA BABU KOMAI A CIKINTA
:
:
:
Cigaban Karatunmu na
Mu'ujizojin Manzon Allah S.A.W
kashi 17
Bismillahir Rahamanir Rahim
wasallallahu alan Nabiyil Karim
:
Bara'u Dan Azib R.A yace mun kasance mu 1400 a ranar yakin Hudaibiyya wata rijiya ce muka yasheta bamu bar komai a cikinta ba Manzon Allah S.A.W yana zauna a bakin Rijiyar ya nemi a kawo masa ruwa da aka kawo masa ya kurkure bakinsa mai Albarka ya tofa Ruwan a cikin Rijiyar Muka zauna Qanqanin Lokaci
ALLAHU AKBAR ai kuwa sai ruwa ya samu a rijiyar muka sha ruwan muka koshi har muka shayar da Dabbobinmu
Imamul Bukhari ya Ruwaito wannan hadisi a babin Yakin Hudaibiyya
:
Allah ya Qarawa ANNABI MUHAMMADU S.A.W wasila da Fadhila fil Jannati Allah ka shayar Damu Ruwan Alkausara bi jahi Sayyidil Wara S.A.W
Ameen
:
Wannan Mu'ujiza ce mai Kara imani ga masu imani mai sanya imani ga marassa imani wadanda Allah ya nufesu da samun Arzikin Duniya da Lahira
:
yaku yan uwana Musulmi yakamata idan aka karanta Mu'ujizar Manzon Allah S.A.W ta samu mukara imani da ganin Girman Manzon Allah S.A.W
:
Ya Allah yakaramana Kaunar Annabi Muhammadu S.A.W Ameen
An Gabatar da wannan Karatu Ranar Litinin 3-5-1438 Hjr

Kukasance damuBerlangganan update artikel terbaru via email:

0 Response to "Gamsassun Mu'ujizozin Annabi (S.A.W)"

Post a comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel